Rassan Kemistiri - Branches of Chemistry

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Rassan Kemistiri


Gabatarwa

Kemistiri yana da rassa da dama, amma akwai jiga-jigai guda biyar waɗanda suke haɗiye sauran. Ga su kamar haka:

  1. Organic Chemistry.
  2. Inorganic Chemistry.
  3. Biochemistry.
  4. Physical Chemistry.
  5. Analytical Chemistry.

Kalli Wannan Bidiyon Domin Ƙarin Bayani

Organic Chemistry
Reshen kemistiri ne da ke nazartar gaurayayyun sinadaran kabon (carbon compounds); sinadaran da ba ƙarfe a cikin su. Shi ke samar da kayayyakin fannonin da suka haɗa da:
(a). Harhaɗa magunguna (pharmaceuticals) da suka shafi sinadaran rigakafi (antibiotics); sinadaran kashe raɗaɗi (painkillers); magunguna (drugs to cure diseases) da sauransu.
(b) Fannin likitanci (medicine), fanni ne da yake nazari tare kuma da fahimtar  cututtuka (diseases); gano jinya (diagnosing diseases) da sauransu.
(c). Fannin abinci (food) fanni ne da yake bincike a kan harkokin abinci da suka haɗa da gano sabon samfurin abinci; gano hanyoyin inganta abinci da sauransu.
(d). Fannin kayan amfanin yau-da-kullum (consumer goods) kamar irin su man gyaran gashi (shampoos); sinadaran canja launin abinci (food dyes): kayan shafe-shafe (cosmetics); sinadaran kashe ƙwari (insect repellents) da sauransu.

Inorganic Chemistry
Fannin kemistiri ne da ke nazartar dukkan abubuwa marasa rai waɗanda basu da sarƙar ko sasarin carbon-hydrogen bond.

Shi ya himmatu wajen lura da makamashin hasken rana (solar power technology); nazarin muhalli (environmental research); harkokin ababen hawa masu inji (automobiles); harkokin wayar tafi-da-gidanka (mobile) da kuma fasahar kwamfuta (computer technology); da sauransu.

Biochemistry
Fannin kemistiri ne da ke da ruwa-da-tsaki a cikin harkokin abubuwa masu rai da kuma sinadaran da ke jikinsu (life and chemical processes in the living organisms).

Shi ne fannin da ke nazaratar cutar kansa (cancer); cututtuka masu yaɗuwa (infectious disease); ƙwayoyin halittar gado (genetics) da sauransu.

Physical Chemistry
Fannin kemistiri ne da ke nazartar siffofin sassan (properties of molecules) da suka haɗa da alaƙar da ke gudana tsakanin ƙwayar zarra (atom) da kuma sassan abubuwa. Wato yana nazartar yadda tsarin sinadaran (chemical structure) abubuwa suke shafar siffofinsu na zahiri (physical properties of substance).

Analytical Chemistry
Rashe ne da ke kula da yadda ake aune-aune da gwaje-gwajen sassan sinadaran (chemical components) mabambantan abubuwan gwaji (samples); wato gwaje-gwajen da suka shafi jini, fitsari, yawu da sauransu. Misali, waɗanne irin sinadarai jinin mai shan sigari yake ɗauke da su?

Fannoni irisu kimiyyar laifuka (forensic science); kimiyyar muhalli (environmental science); gwaje-gwajen magunguna (drug testing) duk suna ƙarƙashin wannan reshen.

Manazarta:


ACS Chemistry for Life (2020). Chemistry Careers. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.acs.org/content/acs/en/careers/college-to-career/chemistry-careers.html

AGCAS (2020). Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/careers-advice/what-can-i-do-with-my-degree/chemistry

AGCAS (2020). Nuclear engineer. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/job-profiles/nuclear-engineer

Better Health (2017). Workplace safety - hazardous substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.betterhealth.vic.gov.au/health/healthyliving/workplace-safety-hazardous-substances

Cleveland Clinic (2018). Household Chemical Products and Their Health Risk An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://my.cleɓelandclinic.org/health/articles/11397-household-chemical-products-and-their-health-risk

Mendeley (2018). Top Ten Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.mendeley.com/careers/article/top-10-chemistry-jobs/

Moore J.T (2020). Ten Great Careers in Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.dummies.com/education/science/chemistry/ten-great-careers-in-chemistry

Tucker L. (2019). What Can You Do With a Chemistry Degree? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.topuniversities.com/student-info/careers-advice/what-can-you-do-chemistry-degree

United States Department of Labor (2020). Chemical Hazards and Toɗic Substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.osha.gov/SLTC/hazardoustoxicsubstances/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub